Wikipedia
| farawa | 15 ga Janairu, 2001 |
|---|---|
| named after | wiki, Insakulofidiya |
| founded by | Jimmy Wales, Larry Sanger |
| ƙasa | Tarayyar Amurka |
| has edition | Wikipedia language edition |
| creator | Jimmy Wales |
| editor | Wikipedia community |
| country of origin | Tarayyar Amurka |
| award received | Princess of Asturias Award for International Cooperation, FSF Award for the Advancement of Free Software |
| owned by | Wikimedia Foundation, Inc. |
| IPA transcription | ˌwɪkɨˈpiːdiə, ˌwɪkiˈpiːdiə, ˌvɪkiˈpeːdia, vi.ki.pe.ˈdi.o |
| operator | Wikimedia Foundation, Inc. |
| product or material produced | Internet encyclopedia |
| platform | LAMP |
| software engine | MediaWiki |
| programming language | PHP |
| bug tracking system | https://phabricator.wikimedia.org/ |
| official website | https://www.wikipedia.org |
| official app | Wikipedia Android app |
| external data available at | https://dumps.wikimedia.org/ |
| Twitter hashtag | Wikipedia |
| license | Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 Unported |
| tarihin maudu'i | history of Wikipedia |
| Dewey Decimal Classification | 030 |
| Stack Exchange tag | https://stackoverflow.com/tags/wikipedia |
Wikipedia wani babban farfajiyar Manhaja ce dake tattare da Mukallolin kundin bayanai akan ilimomi daban daban Dan samar da ilimi ga kowa da kowa, da kara habaka nazarce nazarce, bincike bincike akan ilimomin dake duniya baki daya a kyauta, saboda ganin kowani dan'dam yasamu ilimi batare da biyan wani abu ba.
Wikipedia Shafine dake yanar gizo wanda kowa na'iya shiga kuma ya amfana ko yataimaka dan amfanar da wasu, ta hanyar taimako da ilimi ko gyare-gyare da sauransu, wikipedia tana tattare da harsunan duniya masu yawa, a shafin kowa na iya kirkira tare da gyara makala a kyauta domin taimakawa asamu ilimi daga kowa da kowa, wannan ne yasa wikipedia yayi zarra a duk duniya wurin Samar da ilimi daga asalin inda ilimin yafito Dan kuwa wadanda suka Samar da ilimin ko suke da alaka da ilimin sune ke rubuta ilimin da Kansu, hakane yasa aka ba kowa damar yataimaka da ilimi ta hanyar kirkiran sabon makala ko gyara ta idan anriga an kirkire ta amma bata cika ba ko mai rubuta yayi kuskure. Harwayau babu wani shafi a duniya baki daya daya tattara ilimi da bayanai a yanar gizo a yanzu, kuma miliyoyin dalibai ne da malamai, da sauran mutane suke amfana daga manhajar a kullun.
An kaddamar da shafin Wikipedia ne a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 2001, Jimmy Wales tare da Larry Sanger sune suka hada gwiwa wajen sammar da shafin. A farkon kirkirar shafin an kafa tane da Turanci kadai amma daga baya sanadiyar karbuwa da shafin yayi ne yasa ake samar da karin Harsuna akai akai har zuwa yanzu. A halin yanzu akwai makaloli sama da 5,652,162 a sashen Wikipedia na Turanci wanda kuma shine sashen da yafi kowanne shahara da tarin makaloli. Ayanzu akwai sama da makaloli guda miliyan arba'in a mabanbantan yarurruka 301, sannan shafin ya samu masu ziyara mabanbanta guda miliyan 500 da kuma masu ziyara adadin duka masu ziyara biliyan 18 ko wanne wata tun daga watan Fabrairu na 2014.
A sashen Hausa na wikipedia kuma akwai makalolin da suka kai kusan 2000, duk da yake sashen yana da karancin masu bayar da gudunmuwa amma ahankali sashen yana kara bunkasa cikin gaggawa.